1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kungiyar Taliban ta samu sabon shugaba

Mouhamadou Awal BalarabeMay 25, 2016

Haibatullah Akhunzada da ke zaman mataimakin shugaba ya zama sabon jagora ga 'yan Taliban kwanaki kalilan bayan da Amirka ta halaka tsohon shugaba Mansur.

https://p.dw.com/p/1Itwn
Taliban-Sprecher Sabiullah Mudschahid
Hoto: picture-alliance/dpa

Kungiyar Taliban ta bayyana Mollah Haibatullah Akhunzada a matsayin sabon shugabanta, kwanaki kalilan bayan da sojojin Amirka suka yi nasarar halaka tsohon jagora Mollah Akhtar Mansour. Sannan ta nada Sirajuddin Haqqani da Molah Yaqqob a matsayin mataimakan shugaban kungiyar da ke da tsaurin ra'ayin addini.

Cikin wata sanarwa da Taliban ta watsa ta kafar Internet, kungiyar ta ce majalisar shura da ke zama ta koli ce ta zabi wadannan shugabanni a wani zama da ta yi.

Shi dai Haibatullah Akhunzada da yake kula da fannin shari'a na kungiyar Taliban a baya, ya kasance mataimakin shugaban kungiyar tun shekarar da ta gabata. Shi kuwa Sirajuddin Haqqani, ana danganta shi da wanda ke kitsa hare-haren ta'addanci da ke halaka daruruwan mutane a Afghanistan. Yayin da Mollah Yaqqob kuwa ke zama da ga Mollah Omar, daya daga cikin wadanda suka kafa kungiyar ta Taliban.