Kungiyar Unicef ta kaddamar da kampain ta yaki da cutar AIDS
October 25, 2005mar kare kananan yara, ta Majalisar Dinkin dunia, wato Unicef, ta kaddamar da kampain ta yaki da cutar Aids, da ke ci gaba da bazuwa a dunia mussaman tsakanin kananan yara a nahiyar Afrika.
Shugabar hukumar Unicef Ann Veneman ta kiri taron taron manema labarai, inda ta bayyana mahimman mattakan da wannan Kampain ta kunsa.
A ko wane minti guda , inji Madame Ann ,yaro guda ke mutuwa da cutar Aids a dunia.
A ko wace rana ta Allah kuma, yara kanana yan kasa ga shekaru 15, su dubu 14 ke mutuwa, sanadiyar cutar kabari sallamu allaikum.
Bugu da kari, yara yan shekaru 15 zuwa 24, su dubu 6 ke kamuwa da cutar a kullum sahia.
Jami´ar ta ci gaba da cewa, fiye da yara million 15 su ka zama marayu na uwa ko na uba ko dukka biyun gaba daya,a dalili da cutar kanjamau.
Wannan addadi zai karu zuwa million 18, nan da shekara ta 2010, a yankin kudancin Afrika kadai, inda da dama daga wanda su ka kubuta, su ka ganewa idon su, yada dangi da yan uwa ke mutuwa babu kakabtawa da cutar Aids.
Saidai,duk da tsanani, da bila´in da cutar ke hadasawa, ya zuwa yanzu, kasashen masu hanu da shuni da kungiyoyi kasa da kasa na ci gaba da yi mata daukar sakainan kashi,sun kasa sakka kudade issasu ,domin fuskantar matsalar, inji Madame Ann Veneman.
Daga cikin kashi dari na yara kanana da su ka kamu da Sida kasa da kashi 5 ke samun maganin rage raddadin ta, sannan daga cikin wanda su ka zama marawu, kasa da kashi 10 bisa 100 ke samun tallafi daga ketare.
Daga jimmilar mutanen da ke dauke da kwayar Sida, daya daga ko wane mutum da ke mutuwa yaro ne dan kasa ga shekaru 15, kazalika daya daga ko wane mutum 7 sabin kamu ,karamin yaro ne.
Mahimmin burin wannan sabuwar Kampain da hukumar Unicef ta bullo da ita, shine na kara fadakar da jama´a, a tsawon shekaru 5 masu zuwa, domin shekaru 25 bayan bullowar cutar, ya zuwa yanzu, mutane ba su farga ba da munin ta da kuma illolin ta.
Bugu da kari, Unicef za ta kara matsa kaimi ga kungiyoyin kasa da kasa, da kasashen masu hannu da shuni, domin su kara zuba kuadade masu yawa,don a dukkufa wajen yaki da cutar SIDA.
Kungiyar na bukatar karin a kalla dalla billiard 33 nan da shekaru 5 masu zuwa, na yaki da cutar Aids, ta hanyar jigon a hadi kai a ceci kananan yara, a hada kai a yaki cutar Aids.
A shekara da ta gabata binciken da hukumar ta hukumar majajisar Dinkin Dunia mai kulla da cutar ta gudanar ya gano cewa, fiye da mutane million 39, ke dauke da cutar Aids mafi yawan su a Afrika , duk da dalla billiard 8 da Majalisa ta ware domin yakar cutar, kashi 12 bisa 10 ne kawai na wanda su ka kamu da ita su ka samun magani, mai rage kaifin ta.