Kurdawa a Iraqi sun soki shirin Turkiyya na kutse a yankin su
October 20, 2007Dubbannin kurdawa na Iraqi sunyi cincirin do a iyakar kasar da Turkiyya, don nuna adawar su ga shirin turkiyya na yin kutse izuwa yankin, da sunan cafke tsagerun kurdawa dake kai musu hari.Tare da daga tutoci da kuma rera wakoki, kurdawan sun tabbatar da cewa a shirye suke su kare yankin su, daga duk wani hari da za´a kawo musu. A cewar kurdawan, wannan mataki na Turkiyya, babu abin da zai harfar illa dan da bashi da ido,a cikin kasar ta Iraqi. Tuni dai Faraminista Erdogan na Turkiya ya bukaci gwamnatocin Iraqi da Amurka, dasu rufe sansanin yan tawayen kurdawa dake arewacin kasar.Kiran yazo ne bayan majalisar dokokin kasar ta bawa gwamnati damar yin kutse izuwa yankin na kurdawa ne dake cikin kasar ta Iraqi.Gwamnatin ta Turkiyya dai ta soki lamirin yan tawayen na kurdawa, da kokarin tashin zaune tsaye a cikin kasar su.