Kurdawa na samun nasara kan mayakan IS
October 19, 2014Talla
Mayakan Kurdawa sun samu nasarar korar 'yan kungiyar IS daga mafi yawan yankunan Kubani na kasar Siriya.
Rahotannin sun nunar da cewa ruwan wuta da dakarun Amirka ke jagoranta kan 'yan kungiyar ta IS ya taimaka wa dakarun na Kurdawa. An kwashe makwanni ana wannan fafatawa da tsagerun kungiyar ta IS wadanda ke ikirarin neman kafa daular Islama. Amma duk da ruwan wutar tsagerun na IS sun ki janyewa baki daya.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe