Donald Trump ya fuskanci kakkausar suka daga 'yan Demokrat
August 18, 2020Talla
Michelle Obama da ke jawabi a yayin bude taron da jam'yyar Demokrat ke gudanarwa yanzu haka don tsayar da Joe Beiden da Kamala Harris a matsayin 'yan takarar da za su kalubalanci Donald Trump, ta bukaci Amirkawa da su zabi Joe Beiden a zaben ranar uku ga watan Nuwamban wannan shekara.
Ta ce "A duk lokacin da Amirkawa suka karkata zuwa fadar White House don samun mafita kan wata matsalar, sukan fuskanci rudani da rarrabuwar kai da rashin fahimta" a yayin jawabin da Michelle Obama ta yi na tsawon mintoci 20.
Bangarori da dama dai sun gabatar da jawabansu a yayin taron ciki har da 'ya 'yan jam'iyyar Republican da kuma dangin George Floyd bakar fatar nan da wani dan sanda farar fata ya yiwa kisan gilla a kasar Amirka.