1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Karawa tsakanin Benin da Sudan ta Kudu.

Wudu/ Suleiman Babayo/ LMJMarch 23, 2016

Kungiyar kwallon kafa ta Sudan ta Kudu da ake kira da "Bright Star", ta kammala shirye-shiryen karawa da Jamhuriyar Benin a gasar neman kai wa ga gasar cin kofin kwallon kafa ta Afirka.

https://p.dw.com/p/1IIDV
Kungiyar gasar kwallon kafa ta Sudan ta Kudu
Kungiyar gasar kwallon kafa ta Sudan ta KuduHoto: Getty Images/AFP/H. Kouyate

Yayin da kasar ke cikin hali na rikici mai horas da 'yan wasan yana fatar samun nasara da zai zama abin alfahari ga 'yan kasar. Bilal Felix Komoyangi shi ne mai horas da 'yan wasan Sudan ta Kudu na wucin gadi a karshe mako yayin da suke shirye-shiryen karshe. Gasar ta Sudan ta Kudun da Jamhuriyar Benin dai ta share fage ce domin neman zuwa gasar cin kofin kwallon kafa na kasashen Afirka a shekara ta 2017.

Kungiyar kwallon kafa ta Sudan ta Kudu na karbar horo daga koci Bilal Felix Komoyangi
Kungiyar kwallon kafa ta Sudan ta Kudu na karbar horo daga koci Bilal Felix KomoyangiHoto: Waakhe Simon Wudu

Komoyangi mai horas da 'yan wasan ya ce sun shirya kwarai domin lashe gasar, bayan nasarar da suka samu a kan kasar Equatorial Guinea a watan jiya.

Fatan samun nasara

"A gaskiyya wannan wasa ne mai muhimmanci a wajen mu da kuma duk al'ummar Jamhuriyar Sudan ta Kudu. Yana da matukar muhimmanci kasar da take da shekaru biyar da kafuwa ta shiga gasar neman cin kofin kwallon kafa na nahiyar Afirka."

Duk da wannan fata Komoyangi ya amince da cewa wasan zai zama mai tsauri ga kasar ta Sudan ta Kudu:

"Benin ba kanwar lasa ba ce saboda tana da 'yan wasa da suka fito daga kasashen Turai. Muna da 'yan wasa na gida da waje, wadanda za su nuna kansu a duniya, domin sanin cewar Sudan ta Kudu tana da 'yan wasa na gari."

A karshen watan Disamba na shekara ta 2013 fada ya barke a Sudan ta Kudu, abin da ya jefa kasar cikin halin rashin tsaro. Amma kwallon kafa ya kawo fata tare da dawo da wasu 'yan Sudan ta Kudu zuwa gida. Sudan ta Kudu dai ita ce ta biyu a rukunin C inda take bin bayan Mali da maki uku kawo yanzu. Sannan kasashen Jamhuriyar Benin da Equatorial Guinea suka mara wa Sudan ta Kudu baya. Mali ta doke Sudan ta Kudu a gida da ci biyu da nema, yayin da ita kuma Sudan ta Kudu ta samu galaba a gida kan Equatorial Guinea da ci daya mai ban haushi.

Al'ummar Sudan ta Kudu sun samu kansu cikin halin kunci sakamakon yaki
Al'ummar Sudan ta Kudu sun samu kansu cikin halin kunci sakamakon yakiHoto: Getty Images/AFP/A. G. Farran