Kwamanda na biyu a kungiyar IS ya rasu
March 25, 2016Talla
Babban kwamanda na biyu a rundunar mayakan IS ya bakunci lahira bayan wani lugudan wuta na Amirka a Siriya, abin da ake ganin zai samar da koma baya ga kungiyar kamar yadda rahotanni suka nunar a ranar Juma'ar nan.
Abd ar-Rahman Mustafa al-Qaduli ya rasu ne a cikin wannan wata kamar yadda kafar yada labarai ta Daily Beast da NBC suka nunar. Shashin shari'a dai na Amirka tun da fari ya bayyana cewa zai bada lada na dala miliyan bakwai ga duk wanda ya bada bayanai da suka kai ga kama wannan jigo na kungiyar ta IS.