1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwanciyar hankali ta soma dawowa a jihar Diffa

Larwana Malam HamiJanuary 13, 2016

A Jamhuriyar Nijar, bayan da babban komandan sojojin kasar ya sanar da cigaban da suke samu a yaki da Boko Haram, al'ummar yankin na Diffa ta nuna gamsuwarta da kamarin.

https://p.dw.com/p/1HcV7
Hoto: DW/L. Hami

Daga fara yakin dai a watan Fabareru zuwa 18 ga watan Disamba na 2015 da ya gabata, hare-hare ko dauki ba dadi a kalla 74 ne aka samu tsakanin sojojin kasar ta Nijar da 'yan Boko Haram a cewar rohoton Majalisar Dinkin Duniya. Babban hafsan sojojin kasar Ta Nijar dai janar Seini Garba yayin da yake mika gaisuwar barka da shiga sabuwar shekara ga Shugaban kasa Issoufou Mahamadou, inda yace tabbas zaman lafiya mai dorewa ya sauka a yankin Diffa duk kuwa da ana samun yamutsi lokaci zuwa lokaci da wasu daidaikun 'yan kungiyar.

Nigeria Soldaten in Diffa
Hoto: Reuters/J. Penney

Janar Abdu Kaza da ke a matsayin gwamnan Jihar ta Diffa, shi ma dai ya yaba yadda ake samun dawowar zaman lafiya a yankin Gabashin kasar ta Nijar, yayin da su ma mazauna yankin na Diffa da suka tsinci kansu cikin halin tsaka mai muya suka nuna gamsuwarsu da matakan da gwamnatin kasar ta dauka wanda kawo yanzu suka fara ganin haske a wannan batu na yaki da 'yan ta'addar na Boko Haram.

A yayin da al'umma mazauna Birnin na Diffa da kewaye suka tabbatar da
samun zaman lafiyar, suma dai daga na su bangare kungiyoyin fararen fulla da ke bin diddigin yadda al'amuran ke tafiya kamar su MPCR sun ce hakika wanan batu na dawowar zaman lafiya a yankin na Diffa, ana iya cewar lamurra na ci gaba da daidaita inda jama'a suka soma sakin jiki, tare kuma da gudanar da al'amuran su na yau da kullum babu fargaba kamar yadda suka fuskanta a baya.

Esel an Tränke im Niger
Hoto: DW/Larwana Hami