Kwango: Laifukan yaki a yankin Kasai
July 4, 2018Talla
Jami'in Majalisar Dinkin Duniya na musamman da ke bincike kan abubuwan da suka shafi azabtar da mutane yayin yaki, Nils Melzer ya nunar da cewa rahotannin fyade da yi wa mutane gunduwa-gunduwa da aka samu a yankin na Kasai ka iya janyo kisan kiyashi, inda ya yi gargadin da a dauki matakan da suka dace kafin a sake samun makamancin kisan kiyashin da aka taba fuskanta a kasar Ruwanda. Rahoton na Majalisar Dinkin Duniya da ta fitar da shi bisa rahotannin farko da ta samu daga yankin na Kasai, ya zargi bangarorin da ke yakar juna a kasar na 'yan tawaye da kuma dakarun gwamnati da aikata laifukan yaki da suka hadar da fyade da yi wa mutane gunduwa-gunduwa a cinye namansu.