1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Kwango ta kira jakadanta a Libiya zuwa gida

Gazali Abdou Tasawa MNA
November 22, 2017

Jamhuriyar Demokradiyyar Kwango ta yi kira ga jakadanta a kasar Libiya da ya dawo gida domin nuna rashin jin dadinta da lamarin cinikin bayi da aka bankado ana yi a kasar ta Libiya. 

https://p.dw.com/p/2o1mS
Joseph Kabila Präsident der Demokratischen Republik Kongo
Hoto: picture-alliance/dpa/M. Kappeler

A cikin wata sanarwa da ministan harkokin wajen kasar Léonard She Otekitundu ya fitar a ranar Talata ya bayyana cewa gwamantin na bukatar tattaunawa da jakadan domin sanin takamaiman abin da ke wakana a kasar ta Libiya, da ma duba yiwuwar kwaso 'yan kasar ta Kwango da ke a Libiya zuwa gida idan har ta tabbata cewa suna daga cikin mutanen da cinikin bayin ya shafa a kasar.


Da ma dai Burkina Faso ta kira jakadanta na Libiya zuwa gida a yayin da kasar Nijar daga nata bangare ta gayyaci jakadan Libiya a kasar domin bayar da bahasi, kana Shugaba Mahamadou Issoufou ya yi kira ga kotun kasa da kasa ta ICC da ta duba wannan batu na cinikin bayin a kasar ta Libiya.