Kwararar 'yan gudun hijira zuwa Diffa a Nijar
November 28, 2014Hukumar ta HCR ta ce kame garin Damasak da ke arewa maso gabashin Tarayyar Najeriya mai makwabtaka da Jamhuriyar Nijar da 'yan Boko Haram suka yi a ranar Litinin da ta gabata, ya haddasa kwararar 'yan gudun jihira a kalla 3000 zuwa jihar Diffa a kasar ta Nijar.
Da ya ke magana ga manema labarai a birnin Geneva, Adrian Edwards kakakin hukumar ta 'yan gudun hijira, ya ce wakillansu da ke birnin Diffa a gabashin kasar Nijar, sun sanar musu cewa, 'yan gudun hijirar na ci gaba da kwarara zuwa Nijar din yayin da wasu ke jiran jirgin ruwan kwale-kwale domin ketara ruwan Komadugu Yobe da ke tsakanin kasashen biyu. Dama dai wani dan majalisar dokokin kasar ta Nijar da ya fito daga yankin na Diffa, ya sanar cewa an rufe makarantu da ma asibitoci a gabashin kasar ta Nijar iyaka da Najeriya.
Mawallafi: Salissou Boukari
Edita : Usman Shehu Usman