Labarin Wasanni 07.11.2022
November 7, 2022Dan kasar Kenya, Evans Chebet ya lashe tseren gudun fanfalaki na New York a cikin sa'o'i 2 da mintuna 8 da dakika 41 a jiya Lahadi, lamarin da ya sa kasarsa ta haihuwa zama ta farko da ta lashe dukkanin manyan gasar gudun fanfalaki shida da aka gudanar a wannan kaka da muke ciki. Chebet ya zo gaban Shura Kitata dan kasar Habasha wanda ya zo matsayi na biyu da kuma dan kasar Holland Abdi Nageeye, wanda ya samu lambar azurfa a gasar Olympics ta Tokyo a bara a matsayi na uku.
Wannan dai ita ce nasara ta biyu da dan tsere dan Kenya Evans Chebet mai shekaru 34 ya samu a wannan kakar, baya ga gasar Marathon ta Boston da ya lashe a watan Afrilun da ya gabata. Wannan bajinta ta Kenya, ba a taba ganin irinta ba tun bayan da aka tsawaita manyan tseren fanfalaki na duniya zuwa shida a shekara ta 2013, inda aka kara gudun fanfalaki na Tokyo.
Dan kasar Denmark Holger Rune da ke a matsayi na 18 a duniya, ya ci kofin Master Tennis na farko a birnin Paris inda ya doke wanda ke rike da kofin Novak Djokovic da ci 3-6, 6-3, 7-5. Shi Rude mai shekaru 19 da haihuwa, ya zama dan kasar Denmark na farko da ya shiga cikin rukunin fintattun 'yan tennis 10 da suka fi shahara a duniya tun lokacin da aka kirkiro ATP a 1973.
Wannan dai shi ne wasan Rune wasan karshe na hudu da ya gudu a gasanni hudu na baya-bayan nan da ya halarta, inda ya sha kashi a Sofia, ya lashe gasar Stockholm kuma ya sake yin rashin nasara a Basel. Hakazalika bayan da ya lashe gasarsa ta farko a Munich na Jamus a watan Mayu, Holger Rube ya lashe kambunsa na uku kuma mafi daraja a birnin Paris. Ya kuma zama dan wasa mafi karancin shekaru da ya lashe gasar master ta birnin Paris tun bayan Boris Becker wanda ya zama zakara yana da shekaru 18 a shekara ta 1986.
'Yan matan Mamelodi Sundowns sun tsallake zuwa matakin kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun mata ta CAF a Morocco, bayan da suka doke TP Mazembe da ci 2-0 a wasan rukunin na biyu. Su kuwa 'yan matan Najeriya Bayelsa Queens sun ci gaba da rike matsayi na biyu a wannan rukuni bayan da suka doke takwarorinsu na Wadi Degla na Masar da ci bi 3-0, wanda ya ba su damar cancantar hayewa mataki na gaba na gasar cin kofin zakarun Turai. Wannan dai shi ne karon farko a tarihinsu da 'yan matan Bayelsa suka kai wannan matsayi, wanda ke ba su damar karawa da masu masaukin bakin gasar wato 'yan matan AS Far na Rabat.
A fagen kwallon kafar Jamus, Bayern Munich ta yi abin da ta saba inda ta dare saman teburin Bundesliga da maki 28, bayan da ta samu nasara a kan Hertha Berlin da ci 3-2 a mako na 13 na kakar wasanni. Godiya ta tabbata ga dan wasan Kamaru Eric Maxim Choupo-Moting da ya zura kwallaye biyu da kuma kashi da Union Berlin da a baya ke rike da ragama ta sha tamkar kurar roko a hannun Leverkusen da ci 5-0. Wannan ya sa Union komawa matsayi na uku da maki 26, yayin da Leverkusen da ke fuskantar barazanar zama 'yar baya ga dangi ta murmure daga matsayin na 16 zuwa na 14, lamarin da ya faranta ran mai horaswa Xavi Alonso.
Sai dai a nata bangaren Freibourg da Christian Streich ke horaswa ta yi wa Cologne cin kaca 2-0 , yayin da Borussia Dortmund ta lallasa makwabciyarta VfL Bochum kuma daya daga cikin kurayen baya da ci 3-0 cikin sauki. A yanzu dai Dortmund na a matsayi na hudu da 25, sakamkon kwallaye biyu da Youssoufa Moukoko ya zura, lamarin da yake ganin cewa zai iya bude masa kofar zuwa kofun duniya na kwallon kafa.