Laberiya: Ana gudanar da zaben shugaban kasa
December 25, 2017Talla
A wannan Talata al'ummar kasar Laberiya ke zaben shugaban kasa zagaye na biyu domin tantance gwani tsakanin mataimakin shugaban kasar Joseph Boakai dan shekaru 73 da haihuwa da George Weah dan shekaru 51 tsohon shahararren dan kwallon kafa na duniya.
Masu zabe kimanin milyan 2.2 za su tantance mutumin da zai jagoranci kasar na gaba, inda a karon farko cikin shekaru 70 za a mika mulkin tsakanin gwamnatin demokaradiyya a wannan kasa da ke yankin yammacin Afirka. Duk wanda ya samu nasara zai karbi ragamar tafiyar da gwamnatin kasar ta Laberiya daga hannun Ellen Johnson Sirleaf 'yar shekaru 73 wadda ta zama mace ta farko da aka zaba a matsayin jagora a nahiyar Afirka.