Laberiya: Haramtawa jami'ai fita ketere
February 6, 2017Talla
A karshen makon da ya gabata ne shugabar kasar Laberiya Ellen Johnson Sirlef, ta bayyana kudurin hana wasu jam'ian gwamnatin kasar fita kasashen waje a wani yunkuri na inganta tattalin arziki. To sai dai a wani babi na matakin na cewa shugabar na da ikon baiwa wasu daidaiku alfarmar zuwa ziyara.
To sai dai tuni 'yan kasar ke bayyana mataki bisa yunkuri na kawo sauyi ga halin matsin tattalin arziki da take fama, dama dai tattalin arzikin kasar ta Laberiya na fuskantar koma baya tun bayan da cutar zazzabin Ebola ya barke a shekarun baya.