1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makarantu a Laberiya za su koma aiki

January 6, 2015

Makarantu a kasar Laberiya za su bude a watan Fabarairu mai zuwa bayan kwashe watanni shida a rufe sakamakon annobar cutar Ebola.

https://p.dw.com/p/1EFix
Hoto: picture-alliance/AP Photo/J. Delay

Ofishin ministan ilimin Laberiyan ne ya bada wannan sanarwa a jiya Litinin, yayin da itama hukumar kwallon kafa ta kasar ta bayyana cewa za ta koma fagen fama a ciki da wajen Laberiyan. Sanarwar komawa makarantar dai ta biyo bayan raguwar cutar Ebolan da mahukuntan kasar suka ce an samu, inda kuma suka yi kira ga makarantu da su dauki matakai na tsabta, ta hanyar samar da sabulan wanke hannu masu dauke da magunguna da na'urar auna zafin jiki a dukkan makaratun. A ranar 30 ga watan Yulin bara ne dai shugabar kasar ta Laberiya Ellen Johnson Sirleaf ta bada umurnin rufe makarantu a fadin kasar bayan da cutar Ebola ta dinga yaduwa kamar wutar daji da nufin rigakafin annobar. Kimanin mutane 3,500 ne suka rasa rayukansu sakamakon cutar a Laberiya.

Mawallafa: Salissou Issa/Lateefa Mustapha Ja'afar
Edita: Umaru Aliyu