Lafiya Jari: Matakan karfafa lafiya a Jamhuriyar Nijar
Lafiya
Abdoulaye MamaneJune 10, 2022
Jamhuriyar Nijar da ke yankin yammacin Afirka na kumshe da al'umma miliyan 24, sai dai kwararrun likitoci ba su wuce 1,025 kawai, lamarin da ya gaza ka'idar kowane mutune dubu 100 ya dace su samu kulawar likitoci uku a cikin tsarin Majalisar Dinkin Duniya.