Lakabobin matsin lamba a yaki da sauyin yanayi
Lakabobin fafutikar "Give Earth a Chance" wato "A bai wa muhalli sukuni" wadanda aka yi amfani da su a jerin gwanon kare muhalli na farko a 1970. A wannan lokacin da yakar sauyin yanayi ke kaimi ana samun sabin lakabobi.
'Yajin aikin makarantu don kare muhalli'
Wadannan kalamu da ke rubuce a cikin wannan hoto da Greta Thunberg ke rike da shi na nufin cewa "Yajin aikin makarantu don kare muhalli" an kai rubutun gaban majalisar dokokin Sweden a ranar Jumma'ar watan Nuwamban bara. A lokacin Thunberg na yar shekaru 15, amma a yanzu matakin da ta dauka mai suna "Fridays for Future" ya bazu a duniya karkashin.
'Ba za mu ci kudi ba'
'Yan fafitikar kare muhalli sun datse zirga-zirgar motoci a cibiyar kasuwancin London a watan Aprilun 2019. Inda suka kara da lakabin "Ba za mu ci kudi ba" wanda ya zama abun ambato a yanzu ga bakunan jama'a inda suke sukar jari hujja da ya yi sabani da kare muhalli.
'Idan ku manya ba ku tashi ba to mu za mu yi'
A daidai lokacin da daliban makaranta suka shiga jerin gwano a duniya don yaki da sauyin yanayi, an yi amfani da lakabobi masu yawa wajen gangamin. A wannan jerin gwanon "Fridays for Future" na 15 ga watan Maris, daliban Hong Kong, sun fito cikinsu manya da yara don nuna damuwar kan sauyin yanayi.
'Kin yarda ba tsari ba ne'
Dalibai a Cape Town, Kasar Afirka ta Kudu, suma sun shiga jerin gwanon 15 ga watan Maris cikin jerin gwano kimanin 200 da aka yi a fadin duniya, bisa bangaren dalibai na yaki da sauyin yanayi. Sun rubuta cikin allunan cewa "a daina mutuwa, muhallinmu na mutuwa."
'Makomarmu na cikin tafinku'
Lokacin da kimanin dalibai 25,000 suka fara jerin gwanon 15 ga watan Maris a Berlin na kasar Jamus, sun bullu lakabobi masu yawa. Wadannan masu gangamin sun rubata lakabin "gargadi-gargadi" suna masu daga tafin hannayensu da suka rubuta "Makomarmu na tafinku"
'Babu duniya ta biyu'
Wannan lakabin 'yan fafitika ya samu karbuwa musamman ga Ban Ki moon tsohon sakatare janar na MDD, wanda ya fara furta hakan a taron muhalli na New York a 2014, inda ya ce "There is no plan B because we do not have planet B." wato babu tsari na biyu domin ba mu duniya ta biyu. Kuma a bana an yi ta amfani da wannan lakabi wajen yaki da sauyin yanayi
'Ku yi jerin gwano yanzu ko ku yi iyo an jima'
Wace ta kirkiro jerin gwanon dalibai, Greta Thunberg, ta shiga jerin gwano a Hamburg ranar daya ga watan Maris, 'yan makwanni bayan ta fadawa taron tattalin arzikin duniya a Davos, cewa ina son na rude domin ku ji irin fargabar da nake da ita ko wace rana kuma ina son ku tashi tsaye" Wannnan lakabin ya jawo hankali a Hamburg inda yan fafitika ke kiran a tashin tsaye don yaki da sauyin yanayi.