Lamura na ƙara dagulewa a Sudan ta Kudu
December 29, 2013Rikicin Sudan ta Kudu na ƙara rincabewa, inda rahotanni ke cewa dubban mayaƙa ɗauke da makamai da ke biyayya wa tsohon mataimakin shugaban ƙasar Riek Machar sun dunfari garin Bor.Kamfanonin dilancin labaran ƙasashen yammacin duniya da majiyoyin gwamnati, sun ce mayaƙan da ake kira White Army, 'yan ƙalibila Nuer, waɗanda suke biyayya wa Machar kuma sun kai dubu 25. Wannan lamari ya dakile fata kan sulhunta rikicin.
Ƙasar ta Sudan ta Kudu ta faɗa cikin rikicin ranar 15 ga wannan wata na Disamba, lokacin da Shugaba Salva Kiir ya zargin tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunƙurin kifar da gwamnati. Yanzu duk sassan biyu suna nan da zuwa ranar Talata, domin zama na tattaunawa, bisa shirin sulhu na ƙasashen gabashin Afirka, ko kuma su fuskanci zama saniyar ware. Majalisar Ɗinkin Duniya tana ci gaba da ƙarfafa aikin dakarun kiyaye zaman lafiya domin kare fararen hula. Fiye da mutane dubu sun hallaka tun farkon rikicin.
Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Abdourahamane Hassane