1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Lamura sun kara dagulewa a kasar Sudan ta Kudu

January 8, 2014

Ana ci gaba da kabsa fada cikin yankuna daban-daban na kasar Sudan ta Kudu, yayin da masu shiga tsakani ke neman hanyar shawo kan rikicin

https://p.dw.com/p/1AnG2
Hoto: Reuters

Lamura sun kara dagulewa a kasar Sudan a Kudu, inda kazamin fada ya kaure a wannan Laraba cikin sassa daban-daban na kasar. Wannan yayin da tattaunawar neman magance rikicin ta kakare a birnin Addis Ababa na kasar Habasha.

Wani kakakin 'yan tawaye ya tabbatar da cewa babu maganar tsagaita wuta muddun gwamnatin ta ci gaba da garkame fursunonin siyasa. Tun farko wasu daga cikin masu shiga tsakani sun tsaiguta cewa, maganar sakin fursunonin siyasa da gwamnati ta ki amincewa, ita ce ta janyo rashin samun nasarar kan neman magance rikicin, abin da zai kai ga yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin bangarorin. Dubban mutane sun tsere zuwa sansanonin Majalisar Dinkin Duniya.

Sudan ta Kudu ta tsunduma cikin rikici ranar 15 ga watan jiya na Disamba, bayan da Shugaba Salva Kiir ya zargi tsohon mataimakinsa Riek Machar da yunkunrin kifar da gwamnati, zargin da ya musanta. Kuma yanzu haka 'yan tawaye da ke biyayya wa Machar sun ce suna samun nasara cikin jihohi uku na tsakiyar kasar da ake hakar man fetur.

Mawallafi: Suleiman Babayo
Edita: Saleh Umar Saleh