LARDIN KOSOVO SHEKARU 5, BAYAN AFKA WA SERBIYA DA YAKI DA KUNGIYAR NATO TA YI.
March 24, 2004A jamusance, akwai wani karin magana da ke cewa, gara a kawo karshen wani bala’i da mummunan sakamako, maimakon a ci gaba da samun bala'in har illa ma sha’Allahu. Wannan karin maganar dai, na kwatanta halin da ake ciki a lardin Kosovo shekaru 5 da suke wuce.
Sabili da haka ne, masharhanta da yawa ke ganin cewa, shawarar da NATO da Kungiyar Hadin Kan Turai suka yanke, na kawo karshen manufar siyasar danniya da mahukuntan Serbiya na wannan lokacin ke gudanarwa a lardin Kosovo, daidai ne.
A siyasance dai, wasu bangarori sun sha kira ga yanke wannan shawarar ta yakan mahukuntan tsohuwar Yugoslaviya. Kafin afka wa Serbiyan da yaki dai, kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya, ya zaratad da kuduri, inda ya yi kira ga gwamnatin nshugaba Milosevic, da ta yi duk iyakacin kokarinta, wajen kawo karshen tashe-tashen hankulla da zub da jinin da akke yi a lardin na Kosovo, ta kuma bai wa dimbin yawan `yan gudun hijiran Kosovon, damar komawa matsugunansu.
Sai bayan kwanaki 79, na hadarin bamabaman da jiragen saman yakin kungiyar NATO suka yi ta yi wa kafofin sojin Serbiyan ne shugaba Milosevic ya mika wuya ga sharuddan da kwamitin sulhun ya shimfida masa. Kai tsaye ne kuma, Majalisar Dinkin Duniya ta tsai da shawarar kare yyankin na Kosovo, da bai wa mazauna yankin takaitaccen ‚yancin cin gashin kansu. A ran 10 ga watan Yunin 1999 ne kuma, a wani taron da suka yi a birnin Kolon, ministoocin harkokin wajen kungiyar NATOn da na kungiyar Hadin Kan Turai suka zartad da kudurin tsara shirye-shiryen samad da zaman lafiya a yankin Ballkan gaba daya.
Ta hakan ne kuma dai, kwarjinin Milosevic din ya fara dusashewa. Shekara daya bayan kayen da ya sha a yakin ne kuma, ya sake shan wani kaye a zaben kasar da aka yi. Kusan `yan gudun hijiran Kosovon dubu 80 ne suka koma matsugunansu bayan yakin. Kuma a karo na farko, Albaniyawan Kosovon sun sami `yancin walwala da zama cikin lumana, ba tare da wata fargaba ba.
A bangaren Serbiyawan dai, an yi asarar rayuka da yawa a hare-haren bamabamn da aka kai wa biranen kasar. Kazalika kuma, ffannin tattalin arzikin kasar ya huskanci wani gagarumin koma baya, sakamakon yakin. Kusan Serbiyawa dubu 20 ne kuma aka tilasa musu barin lardin Kosovon bayan yakin. Har ila yau akwai masu tsatsaurar ra’ayi tsakanin Albaniyawan Kosovon. A makon da ya gabata ne dai aka yi wani mummunan rikici a yankin.
Tambayar da masharhanta e yi a halin yanzu dai ita ce: wai shin me aka cim ma a yankin Balkan tun da NATO ta kai hari a Serbiyan k Ga shi dai an dawo gidan jiya, inda wani rikicin kabilanci kuma ya sake barkewa.
Da dai NATO ba ta yi wannan daukin ba, da har ila yau mai yiwuwa a sami dimbin yawan `yan gudun hijiran Albaniyawan Kosovo jibge a sansanoni a Albeniya, da Macedoniya. Shugaban mulkin kama karya Milosevic kuma, da har ila yau yana kan kujerar mulki a birnin Belgrade, maimakon a gidan yarin da yake a halin yanzu a birnin Den Haag. Da kuma wani yakin basasa ya barke a lardin na Kosovo da kasar Macedoniya. Wannan mummunan halin dai babu wanda ke fatar fada wa cikinsa.
Gaba daya dai, masharhanta na ganin cewa, shawarar da NATO ta yanke na yin katsalandan a Serbiyan, ta hana aukuwar wata mummunar annoba, duk da asarar rayukan da aka samu a daukin da dakarun kungiyar suka yi wa Serbiya.