Libiya: AU za ta kwaso bakin haure 20,000
December 7, 2017Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana cewa za ta kara azama a kokari na kwaso al'ummarta da ke gararamba a Libiya. A cewar kungiyar ta na so ta kwashe 'yan Afirka 20,000 da ke a kasar don maida su kasashensu na asali cikin makonni shida da ke tafe.
An dai samu karin matsin lamba kan kungiyar ta AU da ma daidaikun kasashen na Afirka na su je su kwashe mutanensu daga kasar ta Libiya bayan da kafar sadarwar CNN ta bada rahoto kan yadda ake ciniki na bakaken fata a matsayin bayi a wannan kasa da ke a Arewacin Afirka.
Da fari dai Kungiyar AU ta bayyana cewa za ta maido da mutane 15,000 'yan gudun hijira zuwa kasashensu na asali kafin karshen wannan shekara, sai dai ta kara yawan adadi bayan zaman kwamitin kar ta kwana na jami'ai daga Kungiyar AU da Kungiyar EU da Majalisar Dinkin Duniya sun gana a farkon wannan mako.
Tuni dai kasashe irinsu Najeriya da Nijar da Ghana suka fara kwashe al'ummarsu daga kasar ta Libiya don mayar da su inda suka fi kima yayin da ita kuma kasar Ruwanda ta yi tayi na cewa za ta karbi 'yan gudun hijira da suka fiskanci gallazawa a Libiya su 30,000.