1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya da Italiya sun dauki mataki kan cinikin bayi

Ramatu Garba Baba
December 9, 2017

Kasashen Italiya da Libiya sun sanar da kafa kwamiti don lalubo hanyar magance matsalar gwanjon bayi da ya kunno kai dama matsalar nan ta ‘yan cirani da ke anfani da mashigin ruwan Libiya zuwa nahiyar Turai.

https://p.dw.com/p/2p5ll
Marokko Proteste gegen Sklaverei in Libyen
Hoto: Getty Images/AFP/F. Senna

An dai fitar da wannan sanarwar kafa kwamitin ne, bayan tattaunawar da aka yi a tsakanin ministan harkokin cikin gidan Italiya Marco Minniti da Firaiministan Libiya Fayez al-Sarraj. Rahotanni na baya bayan nan sun nuna yadda a kasar Libiya ake sayar da matasa bakar fata a matsayin manoma dama cin zarafin 'yan cirani da suka fito daga kasashen arewacin Afrika masu burin zuwa nahiyar Turai. Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana kaduwa kan rahotannin da suka nuna yadda ake gudanar da cinikin bayi a Libiya batun da ta ce lamari ne mai tayar da hankali.