1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libiya ta fara shirin kawar da IS

Ahmed SalisuApril 28, 2016

Sabuwar gwamnatin hadin kan kasa ta Libiya ta bayyana shirin kafa wata rundunar hadin gwiwa da za ta yi aiki wajen kawar da 'yan kungiyar IS daga kasar.

https://p.dw.com/p/1Iex8
Symbolbild - Flagge ISIS
Hoto: picture-alliance/dpa

Hukumomi a kasar suka ce dukannin sojin gwamnati su kasance cikin shirin gabannin girka rundunar ta hadin gwiwa, kana ta shawarcesu da kada su kai farmaki kan 'yan IS din har sai sun samu umarni daga wannan runduna da ake shirin samarwa.

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya a kasar ta Siriya Martin Kobler ya ce wannan mataki ne da ya dace, inda ya jinjinawa gwamnatin kasar dangane da hakan.

Libiya dai na daga cikin kasashen da 'yan kungiyar IS suka shiga har ma suka maida garin Sirte a matsayn wani dandali na horas da mayakan kungiyar da ke shigarta daga kasashe daban-daban na duniya.