Libiya: Tsagaita wuta tsakanin bangarorin da ke yaki
September 5, 2018Bayan da suka share sama da mako daya suna gwabzawa a kusa da birnin Tripoli, da ta yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 50, bangarorin da ke fada da juna a kasar ta Libiya sun cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yammacin ranar Talata a karkashin jagorancin hukumar samar da zaman lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya a Libiya. Yarjejeniyar wacce ta samu halartar shugabannin sojojin da na kungiyoyin masu dauke da makamai a ciki da kewayen birnin Tripoli da ministan cikin gida na gwamnatin hadin kan kasa wacce kasashen duniya suka amince da ita, ta kuma tanadi kare fararan hula da kiyaye kadarorin gwamnati da kuma sake bude babban filin jiragen saman birnin na Tripoli, wanda yaki ya tilasta rufe shi tun a ranar 31 ga watan Agustan da ya gabata.
To sai dai duk da kasancewar Libiya a nahiyar Afirka take, amma kasashen Turai ne suka yi kane-kane a sahun gaban a duk wani shiri na neman ceto kasar daga bala'in da ta fada kuma su bangarorin da ke fada a kasar suka fi saurara a yayin da shugabannin Afirka da ma Kungiyar Tarayyar Afirka ke zama kusan 'yan kallo a ko yaushe. To wacce fassara za a iya yi wa wannan lamari? Mousbila Sankara tsohon jakadan kasar Burkina Faso ne a kasar ta Libiya na da wannan ra'ayi.
"Ka san kasashen na Turai sune suka kirkiri wadannan kungiyoyi da suka jefa kasar ta Libiya a cikin wannan hali wanda kuma a yau ba wanda ke cin moriyarsa. Domin manyan kasashen duniya irin su Faransa da makamantanta wadanda sune suka haifar da wadannan matsaloli a Libiya, abin da ya fi damunsu shi ne man fetur da Allah ya huwace wa kasar, sauran abin da ke faruwa bai dame su ba. Kungiyar Tarayyar Afirka ce ya kamata ta jibinci lamarin da kanta."
Kasar Libiya dai kasa ce da a yau ke da muhimmanci sosai ga kasashen Turai musamman rawar da take takawa a fannin yaki da kwarara 'yan gudun hijira daga Afirka zuwa Turai. To sai dai abin tambaya shi ne me ya sa shugabannin Afirka da Kungiyar Tarayyar Afirka suka kasa har ya zuwa yanzu yin wani babban tasiri wajen shawo kan rikicin kasar ta Libiya? Wace rawa kuma suke iya takawa a nan gaba wajen ceto kasar? Mousbiha Sankara tsohon jakadan Burkina Faso a Libiya ya amsa yana mai cewa.
"Ba wanda ya ware Afirka, a zahiri ma kusan ba ta cikin duk wani shiri na shawo kan manyan matsalolin duniya. Wannan kuma na da nasaba ne da rashin shugabanni na gari masu karfin fada a ji a duniya. Hasali ma babu jituwa a tsakanin kasashe makobtan juna a yammacin Afirka, makobtansu ma na arewacin nahiyar za ka tarar kasashe kamar Masar da Aljeriya ba sa jituwa da juna saboda sabanin akida. Don haka ina ga babu wani abin da zai sauya haka kawai za a ci gaba da tafiya. Amma Kungiyar Tarayyar Afirka ce ya kamata ta jibinci lamarin da kanta ta tunkari bangarorin da ke rikicin a kasar ta Libiya domin ankarar da su hadarin da matsalar tasu take da ga yankin da ma Afirka baki daya da kuma shawo kansu, kan su zauna domin raba madafan iko da kuma arzikin man fetrur din a tsakaninsu."
Fata a nan shi ne ko illahirin bangarorin da ke fada da juna a kasar ta Libiya za su mutunta a wannan karo yarjejeniyar tsagaitar wutar domin ko a makon da ya gabata sai da suka cimma wata yarjejeniyar mai kama da irin wannan amma ba a je ko ina ba assalatu ta warware suka koma fagen daga.