Jam'iyyun adawar Libiya sun amince da ranar zabe
May 29, 2018Talla
Shugaban kasar Faransa Emmanuel Macron ne ya gayyaci jagororin jam'iyyun hamayyar na Libya don nemo hanyoyin da za a kawo karshen rikicin da aka kwashe shekaru bakwai ana yi a kasar. Tun da fari babban mai ba gwamnatin kasar Libya shawara Taher al-Sonni ya rubuta a shafinsa na Twitter cewar bangarorin jam'iyyun hudun sun cimma matsaya kan kammala tsarin mulkin kasar ta Libya don gudanar da zabe a watan Disamba.