Libya: Hari cikin Masallaci a Benghazi
February 9, 2018Talla
Wasu daga cikin wadanda suka samu raunukan na cikin mawuyacin hali sakamakon hari da aka kai cikin wani masallaci, inda bama-bamai biyu suka tashi a farkon soma sallar Juma'a a masallacin Saad Ibn Abou Abada da ke tsakiyar birnin na Bengazi mai nisan km 1000 a Gabashin Tripoli babban birnin kasar. An dai dana bam din a cikin makara da ke ajiye cikin masallacin, yayin da bam din na biyu aka dana shi a wurin ajiye takalma.