1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Libya: Khalifa Haftar ya bukaci kayan aiki

Salissou Boukari
September 29, 2017

Jagoran sojojin gabashin Libya Marshal Khalifa Haftar ya bukaci tallafin jirage masu saukar ungulu da kuma marasa matuka domin kawo karshen kwararar bakin haure zuwa Turai.

https://p.dw.com/p/2kyaz
Khalifa Haftar
Marshal Khalifa Haftar na LibyaHoto: Reuters

Haftar ya yi wadannan kalamai ne yayin wata hira da aka yi da shi wadda aka wallafa a wannan juma'ar bayan da ya gana da hukumomin Italiya da na Faransa. Marshal Haftar ya ce ya na da tsari wanda zai bada damar tattaunawa da kasashe makwabtan Libya inda bakin hauren ke fitowa.

Sai dai kuma Haftar ya ce idan har kasashen Turai na bukatar a kawo karshen kwarar bakin haure, sai sun taimaka an kawo karshen haramcin da Majalisar Dinkin Duniya ta yi wa kasar ta Libya na shigar da duk wasu kayayyakin da suka shafi harkokin soja a kasar.