1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaki da cutar Ebola a Kongo

Mohammad Nasiru Awal
June 1, 2018

Jaridar Die Tageszeitung wadda ta leka jamhuriyar Demokaradiyyar Kwango ta ce, Lokacin da kwayoyin cutar Ebola ta bulla a birnin Mbandaka duniya gaba daya ta kadu, amma yanzu likitoci sun shawo kan annobar.

https://p.dw.com/p/2yoFV
DR Kongo Ebola Ausbruch
Hoto: Reuters/K. Katombe

Lokacin da kwayoyin cutar Ebola suka bulla a birnin Mbandaka duniya gaba daya ta kadu, amma yanzu likitoci na da kyakkyawan fata, sun shawo kan annobar. Jaridar ta ce wannan babban albishir ne daga kasar ta Kwango inda ta ruwaito wani likita da ke kula da aikin gaggawa kan cutar Ebola na kungiyar agaji ta likitoci wato Medicine Sans Frontier na cewa ko da yake bai zai iya ba da tabbaci lokacin da abin zai auku ba, amma za su dakile yaduwar cutar ta Ebola. Sabanin yadda lamarin ya kasance a yankin yammacin Afirka a shekarar 2014, a wannan karon a Kwango, an yi saurin daukar matakai, inda gwamnati da hukumar lafiya ta duniya suka yi kashedi da wuri, ita kuma gamaiyar kasa da kasa ta yi hanzarin samar da kudin tura kayakin aiki na tan 19 zuwa yankin kurmin na Kwango. Kusan makonni takwas bayan labarin barkewar cutar, ba a kuma kai sati hudu da gwamnatin Kwango ta tabbatar da bullar cutar a hukumance ba, an yi nisa wurin shawo kan lamarin. Mutane 25 daga cikin 51 da suka kamu da cutar suka mutu.

Ana iya maganin kaura daga yankunan karkarar zuwa birane inji jaridar Neues Deutschlnad tana mai cewa kungiyoyin manoma suna samawa mutane albashin da kyakkyawar makoma ta rayuwa a yankunan karkara na kasar Kenya.

M-Farm Preisinformationssystem in Kenia
Manoma na samun sakayya a KenyaHoto: Sven Torfinn/MFarm

Jaridar ta ce Kangocho maimakon Nairobi. Ta ce yayin da dubun dubatan matasa a Kenya ke neman sa'arsu a manyan birane, wani matashi mai suna Jackson Rugara akasin haka ya yi. Yanzu dai ya zama manomi gahawa a kauyen Kangocho. Kimanin shekaru uku da suka wuce ya yi bankwana da birnin Nairobi ya koma kauyen ya fara aikin gona, inda kuma yanzu haka ya kasance babban manomi. Shi dai Jackson Rugara memba ne a wata kungiyar matasa manoma su 14 da ke noman gahawa. Da ribar da suke samu suke ba wa juna bashi don bunkasa sana'arsu, suna sayen shanu da sauran dabbobin kiwo.

Likkafar wani dan kasar Mali ta yi gaba a birnin Paris na kasar Faransa a cewar jaridar Frankfurter Allgemeine Zeitung.

Frankreich Macron trifft Mamoudou Gassama
Faransa ta karrama dan gudun hijira GassamaHoto: picture-alliance/AP Photo/T. Camus

Jaridar ta ce cikin dare daya rayuwar dan ci-rani ta sauya daga bakon da bai da takardar izinin zama cikin kasa zuwa gwarzo da aka karrama shi a Faransa. Wannan dai shi ne tarihin Mamoudou Gassama dan kasar Mali. Jaridar ta ce a wasu kwanaki kalilan da suka wuce dan shekaru 22 da haihuwa ya kan boye da zarar ya hango motar 'yan sanda, amma a ranar Litinin jami'ai ne suka yi masa rakiya zuwa ofishin shugaban kasa Emmanuel Macron wanda ya gode masa bisa bajimtar da ya yi. A ranar Asabar da ta gabata Mamoudou Gassama ya hango mutane sun yi cincirindo a gaban wani gida, wani na rike da wani yaro da ke dab da fadowa, shi kuwa Gassama bai yi wata -wata ba sai ya hau ta bangon ginin benen har hawa na hudu ya ceto yaron. Faransa ta ba shi takardar zama dan kasa da kuma an yi masa tayin aiki da ma'aikatar kwana-kwana.