Maƙarƙashiyar hamɓarar da gwamnatin shugaba Abdoulaye Wade na Senegal
March 19, 2011Hukumomi a Senegal sun ba da sanarwar cafke wasu mutane da ake zargi da yunƙurin shirya wani juyin mulki a ƙasar da sanyin safiyar wannan Asabar.
A wata sanarwar da ministan shari'ar ƙasar Cheikh Tidiane Sy ya fitar, ya ce an cafke waɗanda ake zargin ne domin ciyo kan lamarin kafin ya kai ko-ina. An dai ba da sanarwar kame waɗanda ake zargin ne sa'oi kaɗan kafin al'ummar ƙasar ta ƙaddamar da wata zanga-zangar nuna adawa da gwamnatin Abdoulaye Wade, wanda aka shirya gudanar wa a wannan Asabar, a babban birnin ƙasar wato Dakar wadda kuma ke samun goyon bayan manyan jam'iyyun adawar ƙasar, da ƙungiyoyi masu rajin kare haƙƙin ɗan Adam
Ministan shari'ar dai ya ce hukumomin sun sami rahotannin cewa ƙungiyoyin adawa sun shirya wata manaƙisar da za ta yi sanadiyyar hallakar mutane da dama.
Tuni dai gwamnatin shugaba Abdoulaye Wade ta bada sanarwar ta yi fatali da yunƙurin juyin mulkin wanda da zai kawo ƙarshen mulkin shugaban na tsawon shekaru goma sha ɗaya yanzu.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Mohammad Nasiru Awal