Macky Sall ya lashe zaɓen ƙasar Senegal
March 26, 2012Bayan wata da watani ana tafka mahawarori da cece-kuce a kasar Senegal game da zaben shugaban kasa, a karshe dai kuri'a ta raba gardama,bayan zagaye na biyu da aka shirya jiya tsakanin Abdullahi Wade da Macky Sall.Tun kafin hukumar zabe ta bayyana sakamako a hukunce Wade ya amince da ya sha kaye.
A daidai karfe Tara da rabi ne, na daren Lahadi, a yayin da kafofin sadarwa ke cigaba da bayyana sakamakon zaben, shugaba mai barin gado Abdullahi Wade ya ga alamun ba za shi kai labari ba.Saboda haka ya rungumi kaddara, kuma ba zato ba tsammani, take!!! ya kiri abokin hamayyarsa Macky Sall, domin yi masa barka da arzki kuma.
Wannan halin dataka da da shugaba Wade ya dauka ya ba marada kunya domin jama'a da dama a cikin da wajen Senegal sun yi hasashen cewar kasar zata shiga wani rikicin siyasa bayan zagaye na biyu, inda ake ga alamun dan takara da ya sha kasa zai zargi wanda yayi hanyar da shirya magudi.
Macky Sall ya yi godiya ga Wade
A jawabin farko da ya gabatar Macy sall da ya lashe wannan zabe ya yi yabo da jinjina dantse ga tsofan maigidansa kuma malaminsa wato Abdullahi Wade:
" Babban wanda ya ci nasar a wannan zabe Senegal ce gaba ce gaba daya.Shugaba Abdullahi ya kire ni ta wayar talho domin yayi min barka, na gode masa kwarai.Yanzu abin da ya rage shine gaba daya mu hada karfi domin mu tinkari manyan kalubalen aiyukan ci gaba kasa."
Cemma dai kasar Senegal ta hita zaka a nahiyar Afrika ta fannin mulkin demokradiya, kuma a wannan karo ma ta ba marada kunya.
Mamadu Hudy Diallo, daya ne daga shugabanin jam'iyar PDS ta Abdullahi Wade ,ya bayyana dalilan da suka sa Wade ya amince da kayin da sha ba da bata lokaci ba:Ya ce, mu 'yan kishin jamhuriya ne,kuma 'yan kishin demokradiya saboda haka cilas mun amince da ra'ayin jama'a.
Hakika mun yi yakin neman zabe bil haki da gaskiya, to amma mutum ba shi da tabbas wasu ba su da cikon alkawarin.Yanzu abinda ya ya rage shine mu zauna mu ga inda muka samu kura-kurai, domin mu gyara gaba."
A yanzu haka dai kasashe daban-daban na duniya na cigaba da yabawa kasar Senegal game da wannan zabe, shima shugaban masu sa ido na kungiyar Tarayya Turai Thijs Bermann ya ce cilas a yabawa kasar Senegal:YA ce gaskiya an shirya zaben cikin haske, sannan kafofin sadarawa a kungiyon masu zaman kansu,sun samu cikkaken 'yanci kuma sun nuna kurewa wajen aiki, sabanin kasa makar Ethiopiya da kasashe da dama na Afrika.Ba shakka 'yan Senegal sun yi abun a zo a gani.
A jawabin da ya gabatar shugaban kasar Faransa da ta yi Senegal mulkin mallaka, ya ce ba yi mamaki ba, idan aka yi waiwaye adon tafiya na harakokin siyasar Senegal, amma duk da haka Sarkozy ya ce yaban gwani ya zama cilas.
Ita ma kungiyar tarayya Afrika ta ce ta na cikin murna da halayen da 'yan siyasar Senegal suka nuna, wanda ta yi kira ga sauran kasashen Afrika su dauki darasi.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Mohammad Nasiru Awal