Macron: A kawo karshen mamayar yankin Falisdinawa
December 10, 2017Macron ya ce akwai yiyuwar sake komawa teburin sulhu kan magance rikicin yankin in har an bi a hankali. Macron a jawabinsa a yayin ganawa da Neatanyahu ya soma da yin alla-wadai da rikicin da ya kunno kai a 'yan kwanakin nan a sanadiyar mataki shugaban Amirka Donald Trump kan mayar da Kudus babban birnin kasar Isra'ila.
Shugaban ya jaddadawa Netanyahu kan daukar mataki na kawo karshen mamayar da Isra'ila ke yi a yankin Falisdinawa, abinda ya ce zai kasance ginshiki a kokarin da ake na ganin an samar da zaman lafiya a yankin, Macron ya kara da cewa akwai bukatar yin nazari cikin tsanaki kan tatauna makomar yankin.
Kungiyar hadin kan kasashen Larabawa a na ta bangaren kira ta yi ga Amirka da ta soke matakin bayyana birnin Kudus a matsayin babban birnin kasar isra'ila. Ministocin harkokin kasashen waje na kungiyar ne suka yi wannan kira a wata sanarwa da suka fitar da safiyar wannan Lahadi a karshen taron da suka gudanar a birnin Alkahira na kasar Masar, inda suka yi kira ga kasashen duniya da su bijire bisa matakin kasar ta Amirka.Shugaban Masar Abdelfatah al-Sisi ya mika goron gayata ga shugaban Falisdinawa Mahmoud Abbass don tattauna matakin na Trump.