1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mafita ga rikicin Sudan ta Kudu

December 31, 2013

Tarayyar Afirka ta yi barazanar ladabtar da wadanda ke ingiza yakin cikin gida a Sudan ta Kudu.

https://p.dw.com/p/1AjKY
Flüchtlingen sudan
Hoto: picture alliance/Photoshot

Kungiyar Tarayyar Afirka ta yi barazanar sanya takunkumi akan daukacin wadanda ke da hannu wajen ruruta wutar rikicin Sudan ta Kudu, wanda kuma ke janyo cikas ga kokarin da al'ummomin kasa da kasa ke yi na cimma yarjejeniya da nufin kawo karshen yaki na tsawon makonni biyu kenan, wanda ke neman sake jefa yankin baki daya cikin rudani. Bayan wani taron da Kungiyar Tarayyar Afirka ta gudanar a kasar Gambiya wadda ke yankin yammacin Afirka, AU ta nuna takaicinta dangane da zubar da jinin da ta ce ya zuwa yanzu ya haddasa mutuwar kimanin mutane 1,000. Dama Kungiyar Kasasshen gabashin Afirka ta debarwa masu hannu cikin rikicin na Sudan ta Kudu wa'adin kwanaki hudu, na ko dai su hau teburin sulhu bayan ajiye makamansu, ko kuma su fuskanci fushin kasashen yankin. A kan hakane kwamitin sulhu na kungiyar ta AU ya ce zai dauki dukkan matakan da suka wajaba na ladabtar da wadanda ke janyo cikas ga wannan kokarin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Usman Shehu Usman