Magoya bayan soja sun yi zanga-zanga a Sudan
February 5, 2022Talla
Dubban magoya bayan soja a Sudan, sun sake yin wani gangami a gaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya da ke a Khartoum babban birnin kasar, watanni bayan zanga-zangar nuna adawa da juyin mulki.
Wannan dai na ci gaba da nuna yadda kawuna suka rarraba a siyasar Sudan din, kasar da ke cikin jerin kasashen masu raunin tattalin arziki a duniya.
Wasu daga ciki magoya bayan sojin na Sudan a bisa rakuma, na kalamai ne da ke tir da sa bakin kasashen duniya cikin al'amuran kasar, suna mai da yaba wa sojojin kasar.
Suna dai jaddada goyon bayansu ne a gaban ofishin na MDD, ga jagorancin Janar Abdul Fattah al-Burhan.
Daruruwan 'yan kasar daga wasu sassa ma dai sun isa birnin na Khartoum domin damawa cikin wannan gangamin.