Mahajjata na ci gaba da zuwa birnin Makka
September 18, 2015Duk da matsalar tsaron da ake fama da ita a yankin na Gabas ta tTsakiya, mahajjatan na bana na cike da niya da kuma nutsuwa, inda suke fitowa daga sassa daban-daban na duniya domin gudanar da ayyukansu wanda a hakumance ke fara wa daga ranar Talata mai zuwa. Da yake magana da 'yan jaridu kan batun matsalar tsaro da wasu ke ikirari, Amine Al-Rahmane, wani mahajjaci dan kasar Bangladesh cewa ya yi, "ku duba dubban wadannan mutane, kuna tsammani akwai tsoro a zukatansu", yace "sai dai sabanin haka".
A ranar Alhamis ma dai dubunnan mahajjata ne 'yan yankin kasashen Asiya aka kwashe daga masaukinsu sakamakon wata gobara da ta tashi cikin dare a Hotel din da suke, yayin da tun farko kuma wani mumunan hadari ya haddasa rasuwar mutane fiye da 100 sakamakon fadowar da wani injin daukan kayyakin ginene ya yi.