Saudiyya ta tarbi mahajjatan bana
June 4, 2022Talla
Kamfanin dillancin labaran iqna ya ce kasar Indonesiya ce kasa ta farko da ta sauka a birnin Madina, kuma za ta yi tattaki zuwa birnin Makkah da ke kudancin kasar domin shirin gudanar da aikin hajjin 2022.
An kiyasata mutane miliyan 2.5 ne suka sauke farali a shekarar 2019 gabannin bullar cutar corona a duniya, amma 2020 hukumomin Saudiyya sun ba wa maniyyata 1,000 kacal izinin aikin hajji.
Duk da janye dokar haramta zuwa aikin hajjin saboda corona, hukumomin sun ce duk masu zuwa daga wajen Saudiyya wajibi su nuna shedar ba su dauke da cutar da kuma gwajin yin tafiya wanda bai wuce sao'i 72 ba.