1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Amirka ta wanke Shugaba Trump

February 6, 2020

An kawo karshen dambarwar neman raba shugaban kasar Amirka da mukaminsa, batun da aka yi ta yin dumi kansa a baya-bayan nan. Hakan ya biyo karancin rinjaye ne.

https://p.dw.com/p/3XKze
USA Amtsenthebungsverfahren | Abstimmung
Hoto: picture-alliance/AP Photo/Senate Television

Majalisar dattawan Amirka ta wanke Shugaba Donald Trump daga zarge-zargen neman tsige shi daga mukaminsa a jiya Laraba, abin da ya kawo karshen danbarwar makonni uku na neman raba shi da matsayin, wanda shi ne na uku da ya fuskanci hakan a tarihi.

An dai gaza samun rinjayen da ake bukata ne da zai iya tsige shugaban ne daga bangaren 'yan jam'iyyar Demorats, wanda kuwa ya bai wa Mr. Trump wanda jam'iyyarsa ta Republica ke da rinjaye damar samun nasara.

Jam'iyyar Democrats dai na ci gaba da nuna shakku kan tsarin da majalisar ta bi, bayan amince wa tsige Mr. Trump da ta wakilai ta yi tun da fari.

Suna dai cewa ne an sami karancin shaidu da suka bayyana a gaban majalisar ta dattawa, abin da suka lashi takobin ci gaba da bincike.

An dai sami wani dan jam'iyyar Republica ta Shugaba Trump, wato Mitt  Romney, wanda ya bijire wa jam'iyyar inda ya zabi tsigewa shi.

An zargi Shugaba Trump ne da shiga cikin harkokin majalisa da kuma hada baki da Ukraine kan abokin takarsa, Mr. Joe Biden.