SiyasaJamus
Majalisar Dinkin Duniya ta bukaci daukar mataki a Sudan
December 1, 2024Talla
Shugaban hukumar Mr. Tom Fletcher, wanda ya zanta da 'yan gudun hijira da suka rasa gidajensu, da ke ziyarar kwanaki uku a sansanonin a Sudan da ma kasar Chadi, ya yi alkawarin jawo hankalin duniya domin kawo musu agaji.
Yakin da Sudan ya fara cikin watan Afrilun bara, ya yi ajalin dubban rayukan fararen hula, wasu sama da miliyan 11 kuwa suka rasa muhalli.
Majalisar Dinkin Duniyar dai ta bayyana munin hali na jinkai da Sudan din ke ciki a matsayin mafi muni cikin rikice-rikicen baya-bayan nan.
Karin Bayani: Sudan: Gwamnati na zargin kasashe makobta da agaza wa 'yan tawaye