Majalisar Dinkin Duniya ta soki Kamaru kan 'yan gudun hijira
January 18, 2019Talla
Filippo Grandi wanda shi ne jami'in hukumar 'yan gudun hijira ta Majalisar, ya yi kira ga gwamnatin Kamarun da ta tausayawa sauran 'yan gudun hijirar da suka rage a kasar da matsuguni, ganin barazanar da rayuwarsu za ta fada ciki muddun aka mayar dasu gida yanzu. Jami'in ya ja hankalin kasar kan mutunta dokoki na kasa da kasa kan kyautatawa juna a yanayi irin wannan.
Dubban dubata na 'yan gudun hijira da suka nemi mafaka a Kamaru ne aka mayar dasu Najeriya inji Majalisar. Yan gudun hijira akalla dubu dari uku da saba'in ne ke samun mafaka yanzu haka a Kamaru, kuma dubu dari daga cikinsu sun kasance 'yan gudun hijirar da rikicin Boko Haram ya daidaita a Najeriya.