Majalisar Dinkin Duniya ta ja kunnen Turkiya
May 1, 2017Yayin wani taron manema Labarai ne dai a birnin Geneva, mai kula da kare hakin bil-Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya yi Allah wadai da korar ma'aikata kusan dubu 4 da hukumomin na Turkiya suka yi daga bakin aiki cikin su akwai jami'an ma'aikatar shari'ar kasar dubu 1 guda sannan wasu dubu a fannin jami'an tsaro inda yake cewa "rabin 'yan jaridar da aka aike da su gidan kason, an daure su ne a Turkiya. Wannan abu na damunmu domin kuwa aikin jarida ba laifi ba ne a kasar Turkiya. Wannan matsala dai aba ce da muke ganin ya kamata hukumomi su sanya ido sosai a kanta.''
Tun dai daga yunkurin juyin mulki da aka yi na ranar 15 ga watan Yuli na 2016 kawo yanzu an kama mutane dubu 47 a kasar da ake zargi suna da alaka da sheihin Malamin nan dan kasar ta Turkiya Fethullah Gulen da ke gudun hijira a Amirka.