1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar Dinkin Duniya ta yi suka ga Isra'ila

Halimatu AbbasSeptember 23, 2010

Rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya soki Isra'ila kan harin da ta kai akan jiragen ruwan agaji ga Gaza.

https://p.dw.com/p/PKDE
Mavi Marmara, jirgin ruwan agaji ga zirin Gaza.Hoto: AP

Wani rahoto da komitin kwararru akan kare hakkin bil Adama na Majalisar Dinkin Duniya ya fitar, ya yi nuni da cewa Isra'ila ta karya dokar kasa da kasa, a lokacin da ta kai hari akan ayarin jiragen ruwa da suka yi yunkurin kai kayan agaji zirin Gaza, a watan Mayun da ya gabata. Tara daga cikin 'yan fafutular kare hakkin Falisdinawa suka rasa rayukansu a cikin harin. Komitin ya kira harin da Isra'ila ta kai akan jiragen ruwan tamkar rashin hankali da wuce gona da iri. Rahoton ya kuma yi suka ga Isra'ila game da take hakkin bil Adama . Komitin ya ce takukunmin da Isra'ila ta kakaba wa Gaza ya saba wa doka. Isra'ila ta nuna rashin amincewarta da wannan rahoto . Ta ce sojojinta sun bude wuta ne domin kare kansu a lokacin da suke kokarin tabbatar da biye wa takunkumin.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas

Edita: Umaru Aliyu