Majalisar Dinkin Duniya za ta yi watsi da matakin Amirka
December 17, 2017Talla
Kasar Masar ita ce ta gabatar da wannan kudiri wanda zai yi fatali da matakin na Amirka. Daftarin kudirin wanda manbobi 14 na kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniyar suka amince da shi ya tanadi kushe ikirarn da shugaban na Amirka ya yi tare da hanashi yin tassiri.