Majalisar dokokin Faransa ta amince da Falasɗinu
December 2, 2014Talla
Ƙudirin wanda ba na dole ba ne, wanda masu rinjaye na jam'iyyar 'yan gurguzu da ke yin mulki suka gabatar ya sha suka daga jam'iyyar 'yan mazan jiya.
Hukumar Falasdinawa ta OLP ta yi marhabinn da ƙudrin sannan kuma ta yi kira ga gwamnatin Faransa da ta bi sahu. Tuni da Isra'ila ta bayyana takaicinta a kan wannan yunƙuri, kuma kawo yanzu ƙasashe 135 suka amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cikakken yanci.