1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Wani ya daga tutar Falasdinu a majalisar dokokin Faransa

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
May 28, 2024

Lamarin ya faru ne lokacin da karamin ministan kasuwanci na kasar Frank Riester ke amsa tambayoyi game da halin da Gaza ke ciki

https://p.dw.com/p/4gOMt
Hoto: Alain Jocard/AFP

Majalisar dokokin Faransa ta sanar da dage zamanta, bayan da mataimakin shugaban marasa rinjaye na majalisar Sebastien Delogu ya daga tutar Falasdinu, domin yin izina kan halin da al'ummar Gaza ke ciki na fuskantar hare-haren Isra'ila.

Karin bayani:Kotu ta umarci Isra'ila ta dakatar da yaki a kudancin Gaza

Shugabar majalisar Yael Braun-Pivet, ta ce ba za su amince da irin wannan lamari ba, dalilin kenan da ya sanya ta sanar da dage zaman majalisar na ranar Talata.

karin bayani:Hamas ta amince da tayin tsagaita wuta a Gaza

Lamarin ya faru ne lokacin da karamin ministan kasuwanci na kasar Frank Riester ke amsa tambayoyi game da halin da Gaza ke ciki.

Daga bisani ne jam'iyyar LFI ta marasa rinjayen ta wallafa faifan bidiyon abin da ya faru a majalisar a shafinta na X, tana mai cewar ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen kiraye-kirayen zaman lafiya a ko ina.