1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Majalisar dokokin Nijar ta kammala zamanta

December 2, 2013

Majalisar ta kammala wannan zaman ne ba tare da gwamnati ta cimma burinta na tsige shugaban majalisa Hama Amadou ba

https://p.dw.com/p/1ARz0
Sitzung des Parlaments in Niger foto: DW-Korrespondent Mahamman Kanta, 2.12.2013
Hoto: DW/M. Kanta

Bayan wata biyu da zaman taron majalisar dokokin Nijar, a yau ne aka kammala zaman taron wanda aka tsaida tsarin kasafin kuɗin da gwamnati ta aiko ma majalisar suka zaɓe shi da za a yi aikin ƙasa na shekara da za ta kama sabuwa.

Tsarin kasafin wanda ya tashi kuɗi CFA miliyan dubu sau dubu ɗaya da ɗari takaws da sittin da bakwai, da ɗari biyar da sittin da biyar da 'yan kai.

Wanda za a yi wa ƙasa aiki tsawon shekarar da za ta kama sabuwa.
Shugaban majalisa Hama Amadou, a jawabinsa ya ce an ƙaddamar da wannan tsarin kasafin kuɗin don a yi ma talakawa aiki, inda ya ƙalubalance gwamnati da ta cika alƙawarin da ta ɗauka na kyautatawa talakawa.

Autor: aus Niger unser Korrespondent Mahamman Kanta. Bild nummer 7129 zeigt Parlamentspräsident Hama Amadou (dritte von Links)und sein Stellvertretern.
Shugaban majalisa Hama Amadou da mataimakansa biyarHoto: DW/Mahamman Kanta

"Yana mai farin cikin ƙaddamar da wannan tsarin kasafin kuɗin, inda ya kira 'yan majalisa da su sa ido su ga talakawa sun ci gajiyar wannan tsarin kasafin kudin, kuma su fidda siyasa da son rai".

Na shine ta tambayi dan majalisa Musubahu Musa, dake ɓangaren masu mulki, ana musu zargin 'yan amshin shatan gwamnati.

Da ganin sa matsayinsa na uban iyali goma sha bakwai, ya fi karfin ɗan amshin shata, sai dai yayi ma kasa aiki.

Cece - kuce kan kasafin kuɗin shekara mai kamawa

Amma a na su waje ɓangaren adawa waɗanda ba su zaɓi wannan tsarin kasafin kuɗin ba, a cewar Alhaji Tijani Kadiri, shugaban gungun 'yan majalisar adawa, babu wani kulawa da wannan gwamnatin ke yi ga talakawa, inda ya bada misali ga tsarin kasafin dudin shekarar da ta gabata.

"A wancan tsarin gwamnati ta dauki a za ta saka kashi 25 cikin 100 a aikin bunƙasa ilimi bata yi, haka kiwon lafiya ma bata cika alkawalin da ta ɗauka, ke nan yanzu mahaka ne gwmnati ga fada ba cikawa."

Ita ko kallaba Hajiya Hauwa Abdu Ambali, wadda take ɓangaren masu mulki, takaici ta nuna na idan gwamnati ta tanada ma talakawa taimako to kalilan ke isa garesu. Saboda haka talakawa da wakillan karkara da ƙungiyoyin farar hulla da su hada kai wajen sa ido ga abin da duk wani tallafi da aka tanada musu.

Autor: aus Niger unser Korrespondent Mahamman Kanta. Bild nummer 7155 zeigt Hajiya Hauwa Abdu von der RDP Partei
Hajiya Hauwa AbduHoto: DW/Mahamman Kanta

Sai dai wannan zaman majalisar ya kammala ba tare da cin burin gwamnati, na tsige shugaban majalisa Hama Amadou, yana raba gare da yai da ɓangaren shugaban ƙasa, ya koma wajen adawa, duk da awon zakaran gojin da gwamnati ta yi.

Mawallafi: Mahaman Kanta
Edita: Pinaɗo Abdu Waba