Majalisar Kosovo ta amince da sabuwar gwamnati da aka kafa
January 10, 2008Talla
Majalisar lardin Kosovo da ta ɓalle daga Serbia ta amince da sabuwar gwamnatin da firaminista Hashim Thaci ya naɗa. Ana sa ran gamaiyar jam’iyar tsohon madugun ‘yan tawaye da kuma babbar abokiyar adawarta zasu jagoranci lardin zuwa samun ‘yancin kai daga Serbia cikin ‘yan makonnin nan masu zuwa. Serbia wadda ke shirin gudanar da zaɓen shugaban ƙasa cikin wannan wata,ta na ci gaba da nuna matuƙar adawarta da samun ‘yancin Kosovo. A halin da ake ciki kuma hukumar Taraiyar Turai tace fatar Serbia na sanya hannu kan yarjeniyoyin ciniki da Ƙungiyar Taraiyar Turai ba zai shafi batun ‘yancin lardin na Kosovo ba.