Majalisar Ɗinkin Duniya ta gargaɗi Isra'ila da Siriya
May 6, 2013Ban Ki Moon ya ce; ci gaba da yin tashin hankali tsakanin ƙasashen biyu,na iya zama wata babbar fitina a yankin baki ɗaya wanda yaƙi ya ɗaiɗaita.
A cikin wata sanarwa da ya bayyana babban magatagarda na MDD ya yi kira ga sasan biyu da su yi sassauci tare da kawo ƙarshen kai ruwa rana da ake yi tsakanin kasashen biyu. Hare haren waɗanda su ne na biyu a cikin sao'i 48 da Isra'ila ta kai a Siriya, sun hadasa lallacewar wata cibyar binciken kimiyyar ta ƙasar wacce kasashen duniya ke fargaban cewa cibiyar sarafa makamai ce, masu guba. Isra'ila dai ta ce, ta kai harin ne domin hanna isar da wasu makamai masu linzami da gwamnatin Siriyan ta shirya bai wa mayanan Kungiyar Hezbollah a Libanon da ke makoftaka da Siriyar.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Editan : Yahouza Sadissou Madobi.