Makarantun allo a kasar Senegal
A kasar Senegal ana tilasta wa almajirai na makarantun allo yin bara ana cin zarafinsu ana kuma ci da guminsu.
Dan makarantar allo "Talibes"
Omar Wone dan shekara takwas almajiri ne a wata maratantar allo da a kasar Senegal ake kiransu da "Talibes" wato Dalibai. Omar yana zaune a kan tabarma a makarantar inda a nan yake kuma rayuwa yana koyan karatun Al-Kur'ani a garin Saint-Louis. Omar na fama da ciwon kirji.
Yawon bara maimakon karatu
Bassirou ya ce a rana yana kwashe awa biyar kaca a makaranta yayin da yake kwashe tsawo awa 12 yana yawon bara. "Idan ba mu sami isasshen kudi da za mu koma makaranta mu kwana ba, mu kan kwana a waje don kaurace wa shan duka a makaranta. Ina fushi da iyayena suka bar ni ni kadai a can."
Yi wa malam bauta
Suleiman (hagu) mai shekaru 10 almajiri ne a makarantar allo da abokinsa shi ma almajiri na makarantar Daara, suna bara a kan titin garin Saint-Louis na kasar Senegal. "Ba zan iya zuwa ganin iyayen ba sai na gama makaranta" inji Suleiman. "A kullum ina kai wa malaminmu Francs 200, ko kuma ya lakada mini duka. Sau da yawa ba na samun wannan kudi."
Ana tilasta wa almajirai yin bara
Moussa almajiri ne daga garin Futa, a nan ya debo ruwa a cikin bakin bokiti don yin wanka a harabar kungiyar Maison de la Gare da ke tallafa wa yara a Saint-Louis. "Iyayena sun san ina bara ina ba wa malamina kudin, amma ba sa yin komai a kai. Ba na son yin bara amma an tilasta mini. Ana lakada mini duka idan ban kai kudi ba," inji Moussa.
Bara a cikin yanayi an tsoro
Amadou dan shekaru bakwai, almajirin makarantar allo ne, a hoto nan ya razana da ya ga wata mata lokacin da yake bara a kofar wani shago da ke a garin Saint-Louis na kasar Senegal. Akasari maimakon yaran su zauna makaranta su yi karatu, malamansu na tilasta musu shiga gari yin bara don su kawo musu kudi.
An gudu amma ba a tsira ba
El Hadj Diallo (dama) tsohon dan makarantar allo ne amma yanzu yana tallafa wa yara almajirai su sake sajewa cikin al'umma. A nan yana zantawa da Ngorsek dan shekaru 13 da ke yawon tsintar abinci a kwandon shara. Ya ce ya gudu daga makaranta don ya gaji da yadda malaminsu ke cin zarafinshi yana lakada masa duka. Ya ce shekaru 10 ke nan, abin ya isa haka.
Ci da gumin almajirai na makarantun allo
Mamadou Gueye (na biyu daga dama) malamin yara da ke gararamba a titi da Issa Kouyate (hagu) wanda ya kafa kungiyar Maison de la gare, da ke taimaka wa yaran da ke yawo kan titi sake shiga cikin al'umma. A nan suna wa wani yaro dan shekara takwas rakiya bayan sun ceto shi daga hannun matashin da ke tsakiyarsu yana wa yaron fyade a garin Saint-Louis. Yaron dai dan makarantar allo ne.
Ga takaici ga ban tausayi
Issa Kouyate na kungiyar Maison de la Gare da ke tallafa wa yara almajirai, a nan yana kuka lokacin da yake magana da wani almajiri dan shekaru 8, da ya ceto daga wani matashi da ke lalata da shi, yayin da suke sintiri cikin dare. Yaron dai shi daya ne a waje yana neman wurin kwana lokacin da matashin ya ja shi da karfi. Ya gudu daga makaranta don bai samu isasshen kudin da zai kai wa malam ba.
Tallafi daga tsohon dan makarantar allo
El Hadj Diallou da ke zama tsohon almajiri na wata makarantar allo, yanzu ya zama ma'aikacin kiwon lafiya a kungiyar Maison de la Gare da ke tallafa wa yara almajirai da ke gilo a kan tituna don su sake shiga cikiin al'umma. A wannan hoton yana wa yaran aski don sa musu maganin kurajen da ke fito musu a ka. Yaran dai almajirai ne na wata makarantar allo da ke garin Saint-Louis.
Koyon Karate don kare kai
Demba dan shekaru takwas yana koyon Karate a harabar kungiyar Maison de la Gare. Ya ce yana son ya zama soja don kare al'umma ta kuma zauna lafiya. Demba daya ne daga cikin almajirai a Senegal da malamai ke ci da guminsu. Ya ce suna shan wahala sosai a makarantun allo, iyaye kuma ba ruwansu da halin da 'ya'yansu ke ciki a makarantun allon.