1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Makarkashiyar ta'addanci a yankin Sahel

Gazali Abdou Tasawa
March 28, 2023

Jaridar l'Aube ta Mali ta zargi Faransa da daukar nauyin kungiyoyin 'yan ta'adda a Sahel tare da goyon bayan mahukuntan Nijar batun da ya jawo muhawara a tsakanin kungiyoyin kare hakkin bil Adama a Jamhuriyar Nijar

https://p.dw.com/p/4POLX
Filmstill Dokumentatio Terror im Sahel - Kampf gegen die Dschihadisten
Hoto: Inside the Resistance

 A yayin da wasu jama'a a Jamhuriyar Nijar ke cewa zargin na da kanshin gaskiya, wasu kuma na ganin wata makarkashiya ce ake shiryawa a bisa goyon bayan Rasha domin lalata yunkurin da kasashen biyu na Nijar da Mali ke yi a baya bayan nan na dinke barakar da ke tsakaninsu domin tunkarar yaki da ta'addanci. 

A wani labari da ta buga jaridar l'Aube mai zaman kanta ta kasar Mali ta zargi Faransa da fakewa da biyan kudin diyya na mutanensu da 'yan ta'adda ke garkuwa da su a yankin Sahel, suna zuba wa kungiyoyin makudan kudade don daukar nauyinsu. Jaridar ta kuma zargi shugaba Bazoum Mohammed da hada baki da Faransar a cikin wannan lamari.

Filmstill Dokumentatio Terror im Sahel - Kampf gegen die Dschihadisten
Hoto: Inside the Resistance

Jaridar ta ba da misalin cewa Faransa ta zuba kudi kimanin miliyan goma sha biyu zuwa sha uku na Euro ga kungiyar JNIM reshen Alka'ida a Sahel domin sako dan jaridar kasar ta Faransa Olivier Dubois da Jeffrey Woodke a makon da ya gabata. Da ta ke tsokaci kan wannan zargi kungiyar Tournons la Page ta ce batun Faransa na taimaka wa kungiyoyin yan ta'adda abu ne da suka jima da saninsa.

To amma Malam siraji Issa shugaban kungiyar Mojen na ganin fassara da jaridar take yi wa biyan kudin diyya kabo wadanda aka yi garkuwa da su da cewa daukar nauyin ‚yan ta'adda ne fassara ce ta son kai:DOC

Filmstill Dokumentatio Terror im Sahel - Kampf gegen die Dschihadisten
Hoto: Inside the Resistance

Malam Nassirou Seidou Shugaban kungiyar Muryar Talaka a Nijar cewa ya yi jaridar ta l"Aube da ta wallafa labarin labarin na daga jerin irin jaridun kasar Mali da ke rawa da bazar Rasha a Sahel domin lalata hadin kan kasashen wajen tunkarar matsalar ta'addanci.

Yanzu haka dai a kasashe da dama ana ci gaba da mahawara kan ko matakin biyan kudin diyya ga 'yan ta'adda da kasashe ko daidaikun mutane da aka yi garkuwa da mutanensu ke yi, yana taimaka wa 'yan ta'adda ne ko kuma ceton kai ne musamman ga wanda lamarin ya shafi nashi kai tsaye.