Makomar rikicin Sudan da Sudan ta Kudu
July 7, 2012Ƙasashen Sudan da Sudan ta Kudu, sun yi alƙawarin bada kai wajen samun maslaha kan abubuwan da ke janyo gaba a tsakaninsu. Ko da shike jami'an da suka kasance a wannan tattaunawa da aka gudanar ran asabar, sun ce ɓangarorin biyu basu riga sun rattaba hannu kan yarjejeniyar da zata ƙarfafa wannan alƙawari ba.
Wannan ya zo ne bayan da aka kammala wani zagayen na tattaunawar a babban birnin Habasha kwanaki kaɗan kafin bukin samun 'yancin kan Kudancin Sudan wanda ake sa ran gudanarwa ran litini tara ga watan Yuli.
Ƙasashen biyu sun koma teburin tattaunawar ne ran alhamis bayan da aka tashi babu wani sakamako a makon da ya gabata.
Babban mai shiga tsakani daga Kudancin Sudan Pagan Amum, ya nuna farin cikinsa da wannan cigaba da aka samu, kuma ya ce a taron na gaba zasu tattauna batutuwan da suka haɗa da tsaro, tattalin arziƙi, ciniki da kuma man fetur.
Tsohon shugaban ƙasar Afirka ta Kudu Thabo Mbeki wanda ke jagorantar shirin sulhun na Ƙungiyar Tarayyar Afirka ya yi maraba da wannan cigaban da aka samu.
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu Waba
Edita: Zainab Mohammed Abubakar