1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Sudan bayan kafa gwamnatin rikon kwarya

August 20, 2019

Bayan kawo karshen gwamnatin kama karya ta tsohon shugaban kasar Sudan Omar Hassan Al-Bashir masu ruwa da tsaki na kasar na ci gaba da yin tsokaci akan makomar kasar.

https://p.dw.com/p/3ODhi
Abdalla Hamdok
Hoto: picture-alliance/G. Dusabe

A kokarin samun sahihiyar madogara ta dimukuradiyya domin kawo karshen matsalolin da al'ummar kasar suka fuskanta na tsahon lokaci jama’ar kasar na cigaba da yin tsokaci game da gwamnatin hadaka da aka kafa a kasar.

Samar da gwamnatin hadakar ya zamo wani abin farin ciki matuka bayan amincewa da kundin tsarin mulki na wucin gadi, inda a karshe aka ayyana Abdallah Hamdouk a matsayin shugaban majalisar koli ta wucin gadi a Sudan din. Ko wanene Abdallah Hamdouk?

Abdalla Hamdok, tsohon masanin tattalin arziki ne na Majalisar Dinkin Duniya da ke zaune a Addis Ababa, kuma yayi aiki a ma'aikatu da dama a ciki da wajenn kasar Sudan.

Abdallah Hamdouk ya yi karatu a jami'ar Khartoum, ya samu digirin sa na biyu daga jami‘ar Manchester dake Londan. Yayi aiki a ma'aikatar kudi ta Sudan har zuwa shekarar 1987, daga nan ne kuma ya tafi kasar Zimbabwe a Matsayin mashawarci na musaman har zuwa 1995. Hamdouk ya kuma  yi mataimakin darektan kula da tattalin arzikin Afirka a Majalisar Dinkin Duniya.